Kamfanin AREVA ya dakatar da wasu ayyukansa a Nijar | Siyasa | DW | 02.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kamfanin AREVA ya dakatar da wasu ayyukansa a Nijar

Kungiyoyin ma'aikatan kamfanonin hakar ma'adanai a Jamhuriyar Nijar sun fusata dangane da wannan mataki da kamfanin na AREVA ya dauka.

A jamhuriyar Nijar kungiyoyin ma'aikatan kamfanonin hakar ma'adanai na kasar sun soma nuna hushinsu dangane da wani mataki da kamfanin AREVA ya dauka na dakatar da wasu ayyukansa a cikin kamfanonin hakar Uranium na kasar ta Nijar wato COMINAK da SOMAIR tun daga ranar daya ga wanann wata na Janeru.

Kungiyoyin kwadagon na fassara matakin kamfanin na AREVA da cewa wani yunkuri ne na neman tilasta wa gwamnatin Nijar yin watsi da sabuwar dokar aikin hakar ma'adanai da Nijar din ke son yin amfani da ita a nan gaba cikin huldar cinikayyar da ta hada ta da AREVA. Kuma sun ce a shirye suke su mara wa gwamnatin baya a cikin wanann kokowa tasu da kamfanin na AREVA.

Rashin sabunta tsohuwar yarjejeniya

Da karfe 12 na daren 31 ga watan Disambar shekarar da ta gabata ne dai yarjejeniyar shekaru 10 da ta hada kamfanin na AREVA da kasar ta Nijar cikin aikin Uranium ta kawo karshe ba tare da bangarorin biyu sun cimma wata sabuwar yarjejeniya ba, sabili da wani sabani da ya taso tsakanin gwamnati da kuma kamfanin, dangane da wani matakin da gwamnatin ta dauka na yin amfani da wata sabuwar dokar aikin hakar Uranium wacce ta tanadi karbar wasu kudaden haraji da na Nijar din ta share shekaru a baya tana yafe wa kamfanin. Kuma yau watanni da dama kenan dai da wasu rahotanni ke cewa kamfanin AREVA na yin barazanar dakatar da aikinsa a Nijar domin tilasta wa gwamnatin cin tuwan fashi a kan aniyar tata.

Niger Präsident Mahamadou Issoufou

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

A kan haka ne kamfanin ya dauki matakin dakatar da wasu ayyuka nasa kamar dai yadda Malam Mahammadu Miou, magatakardan kungiyar ma'aikatan kamfanonin ma'adanai ta SYNAMINE reshen garin Arllit ya tabbatar mana ta wayar tarho.

"Production ne wato aikin hakar ma'adanin ne aka tsaida, haka zalika wasu sauran sinadaren da ake hadawa wajen sarrafa karfen na Uranium suma an tsaida aikinsu. Bugu da kari injunan da ke aikin tatar Uranium din su ma an ce kar a tadasu. A takaice dai a halin yanzu duk wadanda ba makanike ne ba ko mai aikin gyaran wuta suna nan suna zaune ne kawai suna jira."

Rahotanni daga kamfanonin hakar ma'adanan na COMINAK da SOMAIR na cewa ma'aikata da dama ne ke dawowa gida tun a tsakiyar rana sabili da rashin aiki. Ita ma dai daga nata bangare babbar kungiyar kwadago ta ma'aikatan kamfanonin hakar ma'adanai ta kasa wato SYNTARMINE ta bakin magatakardanta Malam Inuwa Neino, ta tabbatar da wanan mataki wanda ta fassara shi a matsayin wata barazana da kamfanin na AREVA ke yi ma gwamnatin Nijar domin taka ma ta birki ga aniyarta ta yin amfani da sabuwar dokar aikin ma'adanan ta kasa.

Niger Niamey Proteste AREVA Uran

Zanga-zangar adawa da AREVA a Yamai

"Mun ji Societe sun dauki wata na Janeru sun ce cikin shi ba za a yi production ba har sai an sanya hannu a kan sabuwar yarjejeniya. To mutane su san mafarin tsaida production shi ne Societen AREVA da su na tsammanin cikin watan Janeru suna iya su samu sanya hannu to da yake sun ga ba su sameta ba shi ne ya sa suka fara barazana dan so suke su gama gwamnati da ma'aikatan kwadago shi kuma gwamnatin ya ji tsoro ya dangana da komi."

Babu gudu babu ja da baya

Kungiyar ta SYNTRAMINE ta kuma yi kira ga gwamnatin kasar ta Nijar da kar ta ja da baya a cikin wanann kokowa kuma a shirye 'yan kwadagon kasar suke domin ba ta goyan baya.

"Gwamnati yanda ya kiya to ya tsaya a kan haka dan gwamnati gurinta shi ne talakawanta su ci moriyar arzikinsu ba wai wasu can ba, su zo su tone shi su saida shi su kuma bai wa gwamnati kalilan. A'a kenan gwamnati ya san bisa wannan kokowa za mu kama mashi."

Daga karshe dai kungiyar kwadagon ma'aikatan kamfanonin hakar ma'adanan ta kasar Nijar ta SYNTRAMINE ta yi gargadi ga kamfanin na AREVA kan ya san cewa ko da ya tsaida aiki albashin ma'aikata ba zai yi ko da kwarzane ba a karshen ko wani wata.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin