Areva kamfani ne da ke aiyyukansa na tono ma'adanai da ke karkashin kasa. Nijar na daya daga cikin kasashen da kamfanin ke aikinsa.
Kamfanin ya dau tsawon lokaci ya na aiki na tonon ma'adanin uranium a Nijar din, musamman ma a arewacin kasar. Yanzu haka kamfanin na da rassansa hudu a kasar.