Duk da gaza cimma wata matsaya kamfanin na AREVA ya koma bakin aiki, kuma har yanzu kungiyoyin fararen hula na ci gaba da nuna adawarsu ga aikace-aikacen kamfanin.
A ƙasa da shekaru 40 ƙasar Nijar ta zama ƙasa ta huɗu mai arzikin ma'addanan ƙarfen uranium wanda kuma tun lokacin ƙasar ke zaman jiran tsamani na samun canji na rayuwar al'ummar wadda sama da kishi 60 cikin ɗari na yawan al'ummar miliyan 17 ke yin rayuwa da ƙasa da dala Amirka ɗaya a yini.