Tasirin yarjejeniyar AREVA kan rikicin siyasar Nijar | Siyasa | DW | 27.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tasirin yarjejeniyar AREVA kan rikicin siyasar Nijar

Baya ga rigingimun masu tayar da kayar baya da kasashen Najeriya da Mali da Libiya ke fuskanta, Nijar na cikin wadi na tsaka mai wuya na adawar siyasa.

Ga gwamnatin shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar da ke fuskantar adawa ta kowane bangare a cikin kasar dai, babbar nasara ce kulla sabuwar yarjejeniya tsakaninta da kamfanin makamashi na Faransa watau AREVA a ranar Litinin. Kamfanin dai ya amince da bayar da karin kudaden haraji fiye da wanda ya ke biya a baya. Kazalika zai kuma kashe Euro miliyan 100 wajen zuba jari a ayyukan raya ci gaban wannan kasa da ke yankin Yammacin Afrika.

A fannin tattali dai ana iya cewar wannan babban ci gaba ne ga Nijar, sai dai a fannin siyasa kasar na cikin wani wadi na tsaka mai wuya. Ana ci gaba da kamen wadanda gwamnatin ta kira"masu adawa" wadanda da take zargi da yunkurin kifar da mulki, kamar yadda ministan kula da harkokin cikin gida Massaoudou ya nunar da cewar suna tayar da hargitsi. A karshen makon da ya gabata ne dai aka hana gudanar da zang- zangar jam'iyyun adawa saboda gudun abun da ka iya biyo baya.

A cewar Idayat Hassan ta Cibiyar Nazarin Demokradiyya da ci-gaba a Najeriya da ke makwabtaka dai, kame-kamen da gwamnati ke yi na da nasaba ne da yunkurin yin gangamin adawa:

" Ana ci gaba da kame-kamen duk wanda ake wa kallon mai adawa kuma adawar ba ta tsaya ga jam'iyyun siyasa kadai ba, har ma da kafofin yada labaru da dalibai. Ko kadan babu sassauci dangane da kowane irin adawa a Nijar".

Hama Amadou, Parlamentspräsident in Niger

Hamma Amadou da shugabannin LUMANA

Sama da kashi 60 na al'ummar Jamhuriyar ta Nijar dai na rayuwa ne akan kudi kasa da dala guda a kowace rana, wanda ya sanya MDD sanya ta a jerin kasashe masu fama da matsanancin talauci a duniya. Jama'a na ci gaba da kasancewa cikin bakin ciki da takaici, wanda ya jagoranci adawa da cin hanci, da sa ido kan kafofin yada labaru ga uwa uba karuwar talauci, sannan ga matsalar kame babu kakkautawa.

Kamen da ake yi tun daga karshen mako zuwa yanzu dai na iya tunzura magoya bayan Hamma Amadou, acewar Sebastian Elischer dake bincike akan siyasar kasar ta Nijar a cibiyar GIGA da ke birnin Hamburg anan Jamus:

" Issoufou bashi da magoya baya masu yawa, don haka yana dogaro ne da goyon bayan da yake samu daga Hama Amadou. Tun da wannan tarayya ta lalace, shugaba Issoufou ya samu gurguncewa. Kuma kafa gwamnatin hadin kan kasa da ya yi don ceton gwamnatinsa-ya dada karfafa goyon bayan da Hamma Amadou ya ke da shi a majalisar".

Tun a shekarar da ta gabata ne dai wannan gwagwarmaya ta madafan iko tsakanin shugaban kasa da Hama Amadou da ke shugabantar majalisa ta barke, wadanda suka kasance tamkar tsuntsuya madaurin ki daya a baya. A watan Augustan shekarar ta 2013 ne dai Hamma Amadou da jam'iyyarsa suka rikide zuwa masu adawa da gwamnati, duk da cewar bai ajiye mukaminsa na shugaban majalisa ba.

Symbolbild Afrika Sicherheit im Sahel

Matakan tsaro a sahel

A shekarun 1980 dai Hama Amadou ya kasance mashawarcin shugaban mulkin soji Seyni Kountche, kana ya rike mukamin fraiminista a karkashin gwamnatin Tandja Mamadou. Kafin kifar da mulkin Tandja dai, Amadou na shirin zama wanda zai gaji kujerar tasa, kuma bisa dukan alamu ba gudu ba ja da baya a wannan manufa tasa, acewar masanin kimiyyar siyasa Boubacar Diallo:

" Ya kasance mutumin da ya yi takarar kujerar shugaban kasa a lokuta masu yawa, kuma yana faduwa. Kuma yana kara tsufa ne, amma bisa dukkan alamu yana son lashe zaben na 2016".

Kasar ta Nijar dai na cikin yanayi na gaba kura baya siyaki, ganin cewar fannin tsaro ma tana fuskantar barazana daga kasashe makwabta kamar Mali da Libiya da kuma Najeriya, inda ake ci gaba da shawo kan 'yan gwagwarmaya na Boko Haram. Manazarta sun yi gargadin cewar baya ga 'yan gudun hijira akwai kuma makamai masu yawa da ke kwarara zuwa kasar ta Nijar.

Ana iya sauraron sauti daga kasa

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Pinado Abdu-Waba

Sauti da bidiyo akan labarin