Kalubalen da ′yan jarida ke fuskanta a yayin aikinsu | Siyasa | DW | 02.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kalubalen da 'yan jarida ke fuskanta a yayin aikinsu

Kasar Turkiyya babbar misali ce na inda ake tursasawa 'yan jaridar, inda a wasu kasashe ake jefasu a kurkuku da ma yi musu kisan gilla.

A kasar Turkiyya har yanzu gwamnati na amfani da dokar ta-baci don rufe bakunan 'yan jarida da sauran gidajen buga jaridu masu adawa da ita. Alal misali a ranar Litinin da ta gabata an cafke babban editan jaridar Cumhuriyet da wasu fitattun mawallafa, sannan a lokaci guda an bada samacin kame tsohon babban editan jaridar da yanzu haka yaake a nan Jamus. Sai dai duk matakan tursasawa da hukumomin kasar ta Turkiyya ke dauka kansu, 'yan jaridar sun ce ba za su kasa a guiwa ba wajen gudanar da aikinsu.

Tun bayan samamen da aka kai ranar Litinin a kan gidan buga jaridar Cumhuriyet Murat Sabuncu da wasu editoci akalla 11 na wannan jaridar baya ga matakin rufe rassa 15 na wasu kafafan yada labarai na 'yan adawa, 'yan jarida a kasar ta Turkiyya ke kara fuskantar tursasawa a yanayin gudanar da aikinsu.

Babban labarin da jaridar ta Cumhuriyet ta buga a ranar Talata ta ba shi taken "Ba za mu saduda ba" yayin da ta bar shafin biyu daga cikin marubutanta da aka kame wayam.

Ayse Yildirim marubuciya ce a jaridar ta Cunhuriyet da ta bayanna matakan da ake dauka kan 'yan jaridar a Turkiya da cewa abin kunya ne a fannin demokradiyya da kuma 'yancin yada balarau.

Ta ce: "Abin kunya ne ga demoradiya da 'yancin fadin albarkacin baki a Turkiyya. Yana da muhimmaci a matsayin wani batu na tarihi. Idan muka yi waiwaye a tarihance jaridar Cunhuriyet ta sha fuskanta matsin lamba irin wannan. Sai dai na yanzu wani abu ne dabam da kuma ya kai kololuwa."

Kungiyoyi yada labarai fiye da 160 aka rufe a Turkiyya tun bayan yunkurin juyin mulkin watan Yuli da bai yi nasara ba. Ana zarginsu da alaka da ta'addanci da yada farfagandar kyamar gwamnati. Don mayar da martani wani gungun 'yan jarida da aka kora daga aiki sun kaddamar da wata yekuwa ta shafin sada zumunta don kushe matakan tace labaru da hukumomi ke dauka. Sannan za su ci gaba da ba wa jama'a labaru.

Yanayin aikin 'yan jaridar a Turkiyya batu ne da ya damu duniya baki daya. Amma tsohon babban editan jaridar Cumhuriyet Can Dündar da yanzu haka yake a nan Jamus, ya zargi manyan kasashen duniya irinsu Jamus kawar da ido daga lamarin. To ko su ma kungiyoyin kare martabar 'yan jarida na kasa da kasa na da irin wannan ra'ayi. Christian Mihr shi ne manejan kungiyar 'yan jarida ta kasa da kasa ya yi karin haske a ciki wata hira da tashar DW ta yi da shi.

Ya ce: "Kwarai halin da ake ciki a Turkiyya musamman dangane da 'yan jarida, abin damuwa ne matuka. Tun mako guda da ya wuce halin da ake ciki ya yi muni. Ni kai na na kai ziyara Turkiyya a makon da ya gabata, kuma abinda na tgani a can zan iya kwatantashi da wani yanayi na mulkin kama karya. Bai kamata a zura ido kaiwai ba tare da daukar mataki ba musamman kan wata kasa da ke sha'awar shiga kungiyar tarayyar Turai."

Kungiyar 'yan jaridar ta yi kira ga Jamus da ta saukaka hanyoyin bada bisar gaggawa ga 'yan Turkiyya da gwamnati ke fatattakarsu, dole ne kuma gwamnatin Jamus ta nemi kafafon yada labarun Turkiyya su ba ta jerin sunayen dukkan 'yan jaridar da ake farautarsu. Hakan zai damu gwamnatin Turkiyya wanda kuma zai sa a samu canji mai ma'ana.))

Sauti da bidiyo akan labarin