Kalubalen da rajistar 'yan jam'iyar APC ya fuskanta
February 10, 2014
Kasa da tsawon kwanaki biyar da fara rijistar yayan sabuwar jami'iyyar APC ta adawa, rudanin da ma rikicin cikin gida na neman mamaye shirin da ke zaman irin na farko ga jam'iyar mai neman karbe mulki a kasar.
An dai dauki tsawon lokaci ana shirin, an kuma ma yi masa kallon kafa ta auna farin jinin jam'iyar da ta fito ta kuma ce tana da buri na gyara bisa kura kuran jam'iyar PDP mai mulki. To sai dai kuma daga dukkan alamu tun ba'a kai ga ko'ina ba, ta fara dibar nata kason rikicin an saba ga jam'iyar APC da wani rikicin kokari na danniya ya tilastawa kara lokaci cikin shirin rijistar 'ya'yanta a daukacin kasar ta Najeriya.
A tsakiyar makon jiya ne dai APC ta fara shirin rajistar 'ya'yanta a cikin kasar ta Najeriya, shirin kuma da ke zaman irinsa na farko tun bayan kafa ta cikin tsakiyar shekara ta 2013, da kuma a karkashin jam'iyar ke fatan samun akalla magoya baya miliyan 12 a jihohin kasar 36.
Matsalolin yin rajista a jam'iyar APC
To sai dai kuma an kare kwanaki biyar na farkon fari tare da rigingimu a sassa daban daban na kasar game da yunkurin 'yan jam'iyar na handama da baba-kere a cikin shirin da ke zaman matakin farko na kai wa ga zabe na shugabannin farko cikin watan Afrilun jibi.
Kama daga Yobe zuwa Gombe da Katsina dama Adamawa dai, korafin an sabar ya kaure sararin samaniyar APC bisa tsarin da ya koma kafa ta gwagwarmayar neman ikon jam'iyar a gaba.
Abin kuma da tuni ya fara kai wa ga tsallen murna a bangaren jam'iyar PDP da ke kallon APC a matsayin barazana da kuma ke wa sabon rikicin kallon muguwar rawa da kafa ta hagu a fadar. Barrister Abdullahi Jalo da ke zaman mataimakin kakakin PDP, jam'iyar kuma da ke zargin APC da kokarin aringizon magoya baya da nufin tabbatar da magudi a zabukan badi:
“ Ka ga rajistar nema yanzu a Kano wata mazaba wani yana fadin yawan mutane bai kai 11 ba. Ai ka ga ana ce za a kara takardun zaben, a dole suna zargin kansu cewar wasu suna boye takardun rajistar. Ai na fada maka tusa ba za ta hura wuta ba. Ba yanda za a yi hadaka wani yace ba zai yi kokarin mutanen sa suyi yawa ba, saboda in haka ba ta samu ba to in an zo neman tsaida dan takara za'a samu matsala."
To sai dai koma ya zuwa yaushe ne dai tusar take shirin samar da wuta dai sabbabin rigingimun da ke zaman zakaran gwajin dafi na hadakar dai a fadar APC basu isa kawo matsala dama kila hana ta kaiwa ga cimma burin karbar mulki a badi ba afadar sakataren jam'iyar na kasa Tijjani Musa Tumsah da kuma yace APC tayi tanadi na tabbatar da samar da rajistar ga daukacin 'ya'yanta da ke birane dama kauyukan kasar ta Najeriya:
“ A cikin tsare tsaren da muka bayar da kuma duk 'yan jam'iya suka yarda dashi shi ne ba wanda za'a hanawa rajista ba. Kuma yanzu haka ban ji wani yaje an hanawa rijista ba duk fadin kasar baki daya. Jam'iyar APC jam'iya ce da ke nan. A bude ga duk wani dan Najeriyar da ke fuskantar cewar Najeriya na bukatar canji na kuma bukatar sabuwar alkibla.”
Kokarin shawo kan matsalolin da APC ta fuskanta yayin rajista
To sai dai koma yaya take iya kayawa a tsakanin masu tsintsiyar da kuma abokan hamayar su 'ya'yan lema dai, sannu a hankali dai APC na shirin hawa sawun PDP da ke iya karewa da sababbin mamallaka duk da daukar lokaci da jan kafa wajen aikin rajistar da ke zaman hanya daya tilo na tabbatar da daidaito a tsakanin 'ya'yanta da ke matakai daban daban na kasar a fadar Dakta Umar Ardo da ke zaman wani masanin harkokin siyasar kasar ta Najeriya:
“ Za a ce muna da mutane kaza amma ba za a iya nuna su a kasa ba, tabbas abin da zai faru ke nan. Kuma yadda siyasar ke tafiya in APC ta bada sunan mutumin da zai tsaya mata zabe to dole hukumar zabe ta karba, amma in an bi diddigi bai kamata hakan ta faru ba.”
Abin jira a gani dai na zaman mafita a tsakanin 'yan sai ta sauyan da kuma masu tunanin sai an kara a cikin gwagwarmayar mallakin ruhi dama makomar kasar ta Najeriya yanzu haka.
Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Saleh Umar Saleh