Jawabin Mahamud Abbas a Majalisar EU | Labarai | DW | 16.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jawabin Mahamud Abbas a Majalisar EU

A ci gaba da ziyara da ya kawo a nahiyar turai, yau ne shugaban hukumar Palestinawa, Mahamud Abbas, ya gabatar da jawabi gaban yan majalisar ƙungiyar gamayya turai, a birnin Strasburg.

A cikin jawabin,Abbas ya yi kira, ga ƙasashen turai, su sake duba matakin da su ka ɗauka, na tsuke bakin aljihu ga gwammnatin Hamas.

Y abayana masu dalla dalla matsaloli da Palestinu z ata tsunduiima a ciki muddun turai ta katse agajin da ta ke badawa.

Mahamud Abbas, ya ƙara da cewa, ƙin bada tallafi ga gwamnatin Hamas, zai ƙara hadasa tabarbarewa zaman lahia, a yankin, alhali ƙasashen turai,na daga sahun ƙasashen dunia, da su ka taka rawar gani, ta fannin gina Palestinu .

ƙungiyar gamaya turai a ko wace shekara, na bada gudummuwar dalla million 500, ga hukumar palestinawa.

Tun bayan da Amurika, da EU, su ka yanke shawara ƙin bada wannan kuɗaɗe, a halin da ake cikin yanzu, ma´aikata Palestinu, sun shiga wata na 3, babu albashi.