1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin Ukraine na ci gaba da haddasa tashin farashi a Afirka

Usman Shehu Usman SB
June 10, 2022

Hari kan wani coci da ke garin Owo a jihar Ondo da ke Najeriya ya janyo mutuwar fiye da mutane 50, yayin da ake ci gaba da samun tashin farashin kaya a nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/4CWln
Nijeriya cocin St. Francis lokacin da aka kai hari ana cikin ibada
Cocin da aka kai hari a Owo da ke NajeriyaHoto: Temilade Adalaja/REUTERS

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi sharhin da ke cewa an hallaka masu ibada a cikin mu'jami'a. Inda ta ci gaba da cewa masu ibada sun gamu da ajalinsu a wani coci dake garin Owo a jihar Ondo da ke Najeriya. A lokacin da aka fara yin wa'azin da aka saba yi ranar Lahadi sai wasu dauke da makamai suka kutsa cikin cocin Katholika inda rahotanni suka ce maharan da farko sun shiga mujami'ar a matsayin masu yin ibada kafin suka fara bude wuta kan mabiya sannan suka tarwatsa ababen fashewa. Jaridar ta ce sama da mutane 50 suka mutu yayin da wasu da dama aka garzaya da su zuwa Asibiti..

Harin kan cocin Owo da ke jihar Ondo a Najeriya
Najeriya bayan harin kan cocin Owo da ke jihar OndoHoto: Stringer/REUTERS

Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce yakin Ukraine ya kara haddasa talauci a kasashe kamar Kenya, kasar wace ke kimanin nisan kilo mita 5000 daga Ukraine, amma kuma ana jin radadin yakin, inda farashin kaya ya matukar tashi sama sai kuma wasu kayayyakin da kusan ma ba'a samu. Babban misali shi ne takin noma wanda manoma ke matukar bukata, kuma yanzu farashin takin gona a Kenya ya zama sai mai hali. Don haka jaridar ta ce anan yaki nisan kilo mita 5000 amma kuma radadinsa na isa a kasashe masu na nesa.

Gaisuwa a wajen sayar da kayan abinci
kayan abinciHoto: Channel Partners/Zoonar/picture alliance

A batun da ya shafi radadin yakin Ukraine ga Afirka ita ma jaridar die Tageszeitung ta yi sharhi kan yunkurin kungiyar Tarayyar Afirka AU na ganin an kawo karshen matsalar da aka samu sakamakon yakin na Ukraine. Die Tageszeitung ta ce shugaban kasar Senegal Macky Sall wanda a yanzu ke shugabancin kungiyar Tarayyar Afirka, bayan ganawa da Shugaba Vladimir Putin na Rasha a yanzu Macky Sall ya fahimci matsayin Rasha wajen hana jiragen Ukraine wucewa da kayan abinci. Kuma wannan matsayin da Sall ya dauka ba shi ne kadai ba a nahiyar ta Afirka. Dama tun a watan Aprilu shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya nemi yi wa kungiyar Tarayyar Afirka jawabi ta bidiyo don ya fahimtar da su yananyin yakin da kasarsa ke yi da Rasha, amma a wancan lokacin shugaban kasar Senegal Macky Salla da ke shugabancin Tarayyar Afirka ya ce masa dole sai ya tuntubi shugabannin kasashen Afirka, kuma daga bisa Sall ya ce ya gwammaci ya je kasashen Rasha da Ukraine don sanin matsayinsu abin da kuma ke a ra'ayin shugabannin Afirka da yawa. Bayan ganawa da Putin a wannan mako, Shubaba Sall ya nuna gamsuwar cewa takunkumin da kasashen duniya suka azawa Rasha shi ne sanadin rashin barin abinci ya fice daga Ukraine inda yanzu Rasha ke cilla bama-bamai kan tashar jiragen ruwan Ukaraine, wanda ya tilasta datse jiragen ruwa da ke dakon kaya.

Birnin Kigali na Ruanda inda mata ke aiki a masaka
Mata masu aiki a masana'anta a RuwandaHoto: Kristin Palitza/dpa/picture alliance

Ruwanda ta kasance wata kasa ta daban wannan shi  ne labarin jaridar Neue Zürcher Zeitung. Jaridar ta ce bayan kisan kare dangi da aka yi a shekarar 1994, yanzu Ruwanda ta yi matukar farfadowa kai har ta zarce wasu kasashen Turai wajen ci gaba. Shugaba Paul Kagame da ke jagortantar kasar tun wancan lokacin ya fito ne daga kungiyar 'yan tawaye ya karbi mulkin kasar kuma tun lokacin yake sauya kasar. Jaridar ta kara cewa yanzu bisa alkaluman kungiyar yaki da cin hanci ta duniya wato Transparency International, sun nuna Ruwanda har ta fi wasu kasashen Turai kamar Hungary, Kuroshiya, Girka da makamantansu wajen iya mulki da rashin karbar rashawa. Jaridar ta ce titunan kasar Ruwanda har sun fi na kasar Switzerland tsabta, mace-macen yara da mata wajen haihuwa ya yi matukar raguwa, tattalin arzikin kasar na samun bunkasa ta kashi takwas cikin dari. Sai dai jaridar ta ce babban kalubalen Shugaba Kagame shi ne batun karbar 'yan gudun hijira daga kasashen waje, misali na baya nan wanda ta karbi kudi don tsugunar da 'yan gudun hijran Afirka da ke Birtaniya.