1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libya: Janye mayaka shi ne ginshikin zaman lafiya

Mouhamadou Awal Balarabe
June 23, 2021

Jamus ta karbi bakuncin taron kasa da kasa kan samar da zaman lafiya a Libya wanda ya bukaci janye mayaka da shirya sahihin zabe da nufin samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar ta Arewacin Afrika da ke fama da rikici

https://p.dw.com/p/3vSB1
Berlin Hosts UN Libya Conference
Wakilan taron kasa da kasa kan Libya da ya gudana a Jamus a 2020 Hoto: Getty Images

Mahalarta taron da ke zama irin sa na biyu a kan Libiya sun jaddada mahimmancin shirya sahihin zabe a watan Disamba mai zuwa, da nufin samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar. Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya yi amfani da wannan taro wajen kira da a girmama jadawalin zaben bayan shekaru na mulkin kama-karya da rikice-rikice.

Majalisar Dinkin Duniya da kuma ministocin harkokin waje na kasashen da suka halarci taron, sun bunkaci ficewar dukkan sojojin kasashen waje daga kasar Libya. Ko da shi ma sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken, sai da ya nemi masu ruwa da tsaki da su yi amfani da damar wajen fitar da mayakansu daga kasar don samar da maslaha da za ta share hanyar gudanar da zabe a watan Disamba.

Deutschland Libyen-Konferenz in Berlin
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: Reuters/A. Schmidt

Bisa ga kiyasi da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar, kimanin sojojin haya na kasashen waje 20,000 ne suka kasance a cikin  a watan Disamba na 2020. Har ila yau, manyan makamai na ci gaba da shiga Libiya ba dare ba rana. Sai dai ci gaban da aka samu tun bayan taron farko kan Libiya da Jamus ta shirya, ya sa sakataren harkokin wajen Amirka Anthony Blinken yaba rawar da ta taka.

“Misalin da shugabar gwamnatin Jamus ta kafa, ba wani abin da zai iya fin shi karfi. Kuma taron na yau kyakkyawan misali ne na aikin da Jamus ta yi a kan Libya, da kuma fatan da muke yi na  ganin Libya ta kama hanyar samar da tsaro da 'yanci bisa goyan bayan kasashen duniya.”

Deutschland Libyen-Konferenz in Berlin
Hoto: Reuters/A. Schmidt

Sai dai cikin wani sakon bidiyo da ya aika taron, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya na ganin cewa shirya zabe a fadin Libya abu ne mawuyaci saboda yaki ya daidaita ta. Saboda haka ne ya ce akwai bukatar rikon kwarya domin bai wa 'yan majalisa damar amincewa da dokar da ke tsara zaben.

Roumiana Ougartchinska, dan jarida kuma marubuciyar littafin "Pour la peau de Kadhafi" wanda Ed. Fayard ya buga ya yi tsokaci.

"Batu ne na yunkurin aiwatar da manufar kasa da kasa cewa a gudanar da wadannan zabubbukan. An fara gudanar da zaben farko, bayan faduwar gwamnatin Gaddafi a cikin mawuyacin yanayi. Tabbas ne cewa a lokacin da kuke so, zamu iya. Kuma a lokacin, akwai wata mahaukaciyar mahimmanci. 'Yan Libiya suna da burin bayyana albarkacin bakinsu da kuma zaben shugabanninsu. Abin da aka hana su a yanzu, tsawon shekaru".