1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guterres ya yi kiran hadin kai a Libya

Abdullahi Tanko Bala
January 22, 2020

Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya jinjina wa kudirin da shugabannin kasashen duniya suka nuna na taimakawa shirin samar da zaman lafiya a kasar Libya.

https://p.dw.com/p/3Wcux
Deutschland Libyen-Konferenz in Berlin
Hoto: Reuters/A. Schmidt

Kwamitin ya bukaci bangarorin da ke gaba da juna a kasar su kammala shirin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta. Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Guterres yace wajibi ne a cigaba da yunkurin da ake yi yanzu ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Guterres ya kuma baiyana taron sulhun da aka yi a birnin Berlin wanda shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta jagoranta da cewa wani muhimmin mataki ne musamman kasancewar kasashe 12 sun amince da jadawalin aiwatar da zaman lafiyar da aka gabatar.

Ana fata a karshe kasashen waje ba za su yi katsalandan a rikicin cikin gida na Libya ba tare kuma da martaba haramcin bada makamai ga bangarorin da ke fada da juna.