1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Zanga-zangar adawa da dokokin corona

December 28, 2021

Dubban al'umma a Jamus sun gudanar da zanga-zanga don nuna adawa da tsauraran dokokin annobar corona da gwamnati ta saka domin dakile yaduwarta.

https://p.dw.com/p/44tGg
BG Weltweiter Protest gegen Covid-19 Schutzmaßnahmen
Hoto: Fabian Bimmer/REUTERS

Gwamnatin Jamus dai ta sanya sabbin dokokin haduwar mutane tare da haramta zuwa kallon shagulgula gabanin bukukuwan sabuwar shekara. A makwannin baya-bayan nan ne dai zanga-zangar ta yadu zuwa sassa daban-daban a kasar, sai dai kuma a lokuta da dama ta kan rikide zuwa arangama tsakanin jami'an 'yan sanda da kuma masu zanga-zangar.

Jamus dai na fuskantar barazanar annobar corona a karo na biyar, inda aka samu sabon nau'in cutar mai suna Omicron a jihohin kasar.