Jamus za ta tallafa wa Ukraine | Labarai | DW | 24.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus za ta tallafa wa Ukraine

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta buƙaci da a tsagaita wuta tsakanin gwamnatin Ukraine da 'yan awaren gabashin ƙasar da ke goyon bayan Rasha.

Merkel ta bayyana hakan ne yayin ganawar da ta yi da shugaban ƙasar Ukraine ɗin Petro Poroshenko a ziyarar da ta kai ƙasar. Merkel ta kuma bayyana cewar Jamus za ta bai wa gwamnatin Ukraine ɗin rancenkuɗaɗe har Euro miliyan 500 domin tallafa wa sashen makamashin ƙasar da kuma fannin samar da ruwan sha. Ta kuma ayyana tallafin kuɗin na Euro miliyan 25 domin taimaka wa 'yan gudun hijirar ƙasar.

A jawabinsa Shugaba Petro Poroshenko na Ukraine ɗin ya godewa shugabar gwamnatin ta Jamus bisa wannan tallafi. Kawo yanzu dai ana ci gaba da yin zaman doya da manja tsakanin gwamnatin ta Ukraine da kuma 'yan awaren gabashin ƙasar da ke goyon bayan Rasha kuma suke barazanar ɓallewa.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdorahamane Hasane