1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus za ta dauki 'yan gudun hijirar Ukraine

March 6, 2022

Mahukuntan na Jamus sun ce za su dauki 'yan hijirar ba tare da la'akari da launin fata ba a yayin da ake ci gaba da zargin yadda aka nuna wa bakaken fata wariya a lokacin da jama'a ke rububin ficewa daga Ukraine.

https://p.dw.com/p/4855x
Berlin |Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz
Hoto: FABRIZIO BENSCH/REUTERS

Jamus ta sanar da cewa za ta karbi 'yan gudun hijira daga kasar Ukraine. Ministar harkokin cikin gida Nancy Faeser ce ta sanar da haka a cikin wata tattaunawa da ta yi da jaridar Jamus ta mako-mako da ke fita ranar Lahadi ta Bild am Sonntag.

Ministar ta ce Jamus na son ceto rayukan mutanen da ke neman taimako, a don haka za ta karbi duk mutumin da ya fito daga Ukraine ko da kuwa ba dan kasar ta Ukraine ba ne. 

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane miliyan daya ne suka tsere daga Ukraine domin guje wa tashin hankalin da ya biyo bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.