1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta kara mayaka 5000

November 26, 2018

Jamus za ta yi kokarin cike gibin mayaka da ta samu bayan wani lokaci mai tsawo

https://p.dw.com/p/38wed
Fußball 2. Bundesliga Karlsruher SC Dynamo Dresden  Fans von Dynamo Dresden
Hoto: Imago/Jan Huebner

Hukumomi a nan Jamus sun bayyana shirin da gwamnati ke yi na kara yawan dakarun kasar akalla 5000 adadin da ya zarta wanda aka yi hasashe tun farko.

Ministar harkokin tsaron Jamus, Ursula von der Leyen, ta ce idan aka yi hakan dakarun kasar za su kai dubu 203 a nan da shekara ta 2025.

Da ma dai akwai bayanan da suka tabbatar da samun gibi daga yawan mayakan da Jamus ke da su, musamman bayan karshen yakin cacar baka

Sai dai akwai wasu daga cikin 'yan kasar wadanda ke shakku kan yadda za a yi a sami damar cike gibin da aka samu daga shekarun da suka biyo bayan yakin.