Jamus za ta janye sojojinta daga Turkiya | Labarai | DW | 07.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus za ta janye sojojinta daga Turkiya

Gwamnatin Jamus ta yanke shawarar janye sojojinta da ke girke a cibiyar sojojin Incirlik ta kasar Turkiya domin mayar da su a kasar Jodan.

Gwamnatin Jamus ta dauki matakin janye sojojinta da ke girke a cibiyar sojojin Incirlik ta kasar Turkiya domin mayar da su a kasar Jodan. Ministar tsaron kasar ta Jamus Ursula Von der Leyen ce ta sanar da hakan a karshen taron majalisar ministoci na wannan Laraba tana mai cewa:

"Kasancewa gwamnatin Turkiyya ta ki bai wa 'yan majalisarmu izinin ziyartar cibiyar sojojin ne, majalisar ministocin ta ba da shawarar dauke dakaran gwamnatin Jamus din daga cibiyar ta Incirlik zuwa kasar Jodan"

Yanzu dai kasar ta Jamus za ta maida da sojojin nata 260 a cibiyar sojojin Azraq ta kasar ta Jodan tare da kayan aikinsu da suka hadada jiragen yaki da kontina 200 na kayan aiki. A tsawon lokacin da aikin jigilar sojojin da kayan aikinsu zai dauka ,jiragen jigilar kaya aiki da na leken asiri na kasar ta Jamus za su dakatar da bayar da gudunmawarsu ga rindunar kawancan kasa da kasa da ke yaki da Kungiyar IS. 

Wannan mataki dai na kara tabbatar da tabarbarewar dangantakar kasashen biyu na Jamus da Turkiyya wace ta samo asali daga zargin da mahukuntan Turkiyar ke yi wa Jamus na bayar da mafakar siyasa ga wasu sojojin Turkiyyar da ke da hannu a yin kurin juyin mulkin da ya ci tura a aksar a shekarar bara.