Jamus za ta aika sojojin 1,200 don yakar IS | Labarai | DW | 01.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus za ta aika sojojin 1,200 don yakar IS

A wannan Talatar nan ce majalisar zartawar gwamnatin Jamus ta amince da tura dakarun a kawancen da kasashe suke na hada rundunar da za ta yaki kungiyar IS da ke a Siriya.

Majalisar ministocin ta dauki matsayin ne domin tallafawa Faransa da kuma kasashen da ayyukan kungiyar IS ya shafa, a inda tallafin ya hada da jiragen yaki da kudade.

A cewar ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier, suna yin duk abinda ya wajaba ne, ta fuskar matakan soji domin tinkarar ayyukan kungiyoyin ta'adda.

Amincewar dai na yin nuni da cewar Jamus ta amsa kiran Faransa kan tallafin da take nema, don dakile ayyukan kungiyar IS da ta kai hare-hare a birin Paris kwanakin baya.