1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan wasan kwallo a Jamus sun kamu da cutar Coronavirus

Zulaiha Abubakar
May 4, 2020

Hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta kasar Jamus wato DFL ta ce 'yan wasan kwallon kafa 10 ne da ke bugawa a gasar Bundesliga ta daya da ta biyu aka tabbatar sun kamu da cutar Coronavirus ya zuwa yanzu.

https://p.dw.com/p/3bllC
Fußball Bundesliga Logo
Hoto: Getty Images

 A sanarwa da ta fita a wannan Litinin Hukumar ta DFL ta ce ya zuwa yanzu an gudanar da gwajin ne kan 'yan wasa 1724, wato 'yan wasa 18 a kowace daga cikin kungiyoyi 36 na Bundesliga ta daya da kuma ta biyu. Sai dai hukumar ta DFL ba ta bayyana sunayen 'yan wasan da suka harbu da cutar ta COVID-19 ba ko kuma kungiyoyin da suke buga wa wasa ba.

Sai dai tun a ranar Juma'ar da ta gabata kungiyar FC Kolon ta sanar da cewa uku daga cikin 'yan wasanta sun kamu da cutar. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar kula da wasannin kwallon kafar kasar ta Jamus ke tunanin komawa wasannin na Bundesliga a tsakiyar wannan wata na Mayu domin kammala kakar wasannin shekarar bana.