Jamus: Yan sanda sun dakile yunkurin hari | Labarai | DW | 31.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Yan sanda sun dakile yunkurin hari

Jami'an tsaro a Jamus sun tsare wani matashi mai shekaru 19 bisa zargin shirin kai harin ta'addanci a da nufin hallaka dumbin jama'a a Jamus.

Yan sandan Jamus sun kama wani matashi dan Siriya mai shekaru 19 da haihuwa da yunkurin kai harin ta’addanci.

Ofishin mai gabatar da kara na tarayya yace matashin ya kudiri aniyar aikata ta’asar ce da nufin hallaka mutane da dama.

Wata sanarwa daga mai gabatar da karar ta ce mutumin wanda aka kama mai suna Yamen A. yanke shawarar aikata wannan danyen aiki ne tun a cikin watan Juli na wannan shekarar inda yake da niyyar tada bama bamai domin Jamusawa da yawa.