Jamus ta nemi hadin kai a tsakanin Turai da Afirka | Labarai | DW | 21.11.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta nemi hadin kai a tsakanin Turai da Afirka

Shugaba Frank-Walter Steinmeier, ya nemi hadin kai a tsakanin kasashen Turai da Afirka a ziyarar farko da wani shugaban kasar zai kai a kasar Afirka ta Kudu a cikin shekaru 20.

Shugaban ya tabo batutuwa da suka kunshi yaki da cutar HIV da matsalar fari da sauyin yanayi ke haifarawa. Wannan ziyarar wani tubali ne na ingantuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Daga shekara ta 2019 Afirka ta Kudun da Jamus za su cigaba da zama membobi a kwamitin sulhu na MDD, dangane da haka ne Steinmeier ya bayyana alakar kasashen biyu a matsayin abu mafi dacewa.Baya ga Afirka ta Kudu, Steinmeier ya ziyarci kasar Botswana.