1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta musanta tallafawa kisan kare dangi a Gaza

April 11, 2024

Shugaban gwamnatin Jamus Olafz Schölz na fuskantar matsin lamba ta katse tallafin da yake ba wa Israila a yakin da ta ke yi da Hamas. Shugaban ya kafe akan cewa bisa ka'ida yake gudanar duk wani aikin tallafawa Israila.

https://p.dw.com/p/4ee7N
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netenyahu da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a birnin Berlin
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netenyahu da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a birnin BerlinHoto: Christian Mang/REUTERS

Schölz na fuskantar matsin lamba ne ta fuskar shari'ah dangane tarin kararrakin da aka shigar gaban kotunan Jamus kan rawar da yake takawa a yakin Gaza.

Karin bayani: Jirgin yakin ruwan Jamus ya nufi Bahar Maliya

Bayan shafe lokaci mai tsawo suna zanga-zangar adawa da manufofin Schölz kan Gaza, masu boren sun canza salo wajen shigar da kara kotu domin kalubalantar matakin ta fuskar shari'ah ko za su yi galaba wajen sauya matakin majalisar dokokin Jamus na amincewa da kudurin shugaban gwamnatin na Jamus.

Karin bayani: Jamus ta yi kira ga Isra'ila ta kauce wa take hakkin 'dan adam a Gaza 

Masu shigar da karar na zargin Jamus da amfani da tallafin makamai wajen tallafawa kisan kiyashi a Gaza, Wanda hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa da kare hakkin 'dan Adam.Tuni shugaban gwamnatin na Jamus ya musanta zargin tallafa Isra'ila da nufin ingiza kisan kiyashi a Gaza.