Jamus ta mika wa Namibiya sauran Kwarangwal | Labarai | DW | 29.08.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta mika wa Namibiya sauran Kwarangwal

Jami'an ma'aikatar raya al'adun kasar Namibiya sun karbi sauran kasusuwan kwarangwal na 'yan kasar da aka kashe domin gwajin kimiya a zamanin mulkin mallaka.

Ministar raya al'adun Namibiya Katrina Hanse-Himarwa ce ta jagoranci tawagar birnin Berlin, inda aka mika kokunan kan mutane 16 da sauran wasu kasusuwa da aka kawo su Jamus domin gudanar da binciken kimiya.

An kiyasta akalla 'yan kabilar Hiroro da Nama dubu 65 aka kashe yayin zanga-zangar neman 'yanci daga turwan mulkin mallaka a shekarar 1904 da 1908. Wannan dai shi ne karo na uku da Jamus ke mayarwa gwamnatin Nambiya kasusuwan mutanensu da suka mutu a Jamus bayan da aka kawo su da rai don gwajin kimiya.