An karfafa tsaro kan iyakar Jamus
September 9, 2024A wannan Litinin hukumomin Jamus sun karfafa matakan kan iyakokin kasar domin dakile bakin haure daga shiga ta hanyar da ta saba ka'ida, bayan hare-haren da kasar ta fuskanta daga masu kaifin kishin addinin Islama, inda tuni hare-haren suka haifar da fusata daga al'umma, yayin da gwamnatin ta kasance karkashin matsin lamba na daukan matakan magance matsalolin kwararar bakin haure zuwa kasar.
Karin Bayani: Scholz: Za mu tsaurara doka kan hari da wuka
Karkashin matakan da aka dauka na wani lokaci, ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta ba da umurnin karfafa bincike a daukacin iyakokin kasar ta Jamus, domin tabbatar da dakile masu kaifin kishin addinin Islama da ke aikata miyagun laifuka cikin kasar. Shi kansa shugaban gwamnatin ta Jamus, Olaf Scholz yana karkashin matsin lamba kan daukan matakan da suka dace na dakile shigar bakin haure cikin kasar, bayan hare-haren na masu kaifin kishin addinin Islama.