Jamus ta kame ′yan Nazi sama da 200 | Labarai | DW | 12.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta kame 'yan Nazi sama da 200

Hukumar 'yan sandan kasar Jamus ta kame akaala mutane 211 wadanda suka kona motoci dama farfasa gilasai a birnin Leipzig a lokacin wata zanga-zangar da suka gudanar a jiya Litinin.

Hukumar 'yan sandan ta bayyana cewa jami'anta biyar sun ji rauni a cikin lamarin na birnin Leipzig, a yayinda wasu bakwai suka ji rauni a lokacin kwantar da tarzomar. Irin wannan zanga-zanga da ta gudana a ranar Lahadi a birnin Potsdam na gabashin kasar ta Jamus inda ta kai 'yan sanda yin arangama da masu zanga-zangar.

Kasar Jamus wacce ta yi rijistan masu neman mafaka sama da miliyan guda a shekarar 2015, na fiskantar karuwar ayyukan tsageranci wadanda ake dangantawa da Kungiyoyin 'yan Nazi.

Haka zalika kasar na cikin juyayin cin zarafin daruruwan mata da wasu mazajen 'yan asalin kasashen Arewacin Afirka da na yankin Gabas ta Tsakiya suka aikata a jajibirin sabuwar shekara ta 2016 a birnin Kolon