1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta hana Facebook samun bayanai daga WhatsApp

Mouhamadou Awal Balarabe
May 11, 2021

Wata hukumar kare bayanan ta kasar Jamus ta umarci kanfanin Facebook da ya dakatar da shirinsa na amfani da bayanan da kamfanin WhatsApp ke samar masa, bayan da ya sauya dokokin sirii da ake ta cece-kuce a kansa.

https://p.dw.com/p/3tGLV
Symbolbild I Whatsapp I Coronavirus I Indien
Hoto: Santarpan Roy/ZUMA/picture alliance

A cikin wata sanarwar da ya fitar a birnin Hamburg, shugaban hukumar kare bayanai ta Jamus Johannes Caspar ya ce, "ya bayar da umarnin ga reshen Facebook na Ireland don yana tatsar bayanan daga WhatsApp ne don amfanin kansa ".

Sai dai a wani martani da ya aika wa kamfanin dillacin labarai na AFP, WhatsApp ya tabbatar da cewa wannan umarnin ya nuna rashin fahimtar sabbin dokoki, saboda haka ba zai yi tasiri a kan shirin sabunta dokokin WhatsApp na sirin bayanai ba.

Wannan dakatarwar za ta yi aiki har tsawon watanni uku, kuma hukumar kare bayanan ta Jamus ta yi barazanar gabatar da karar a gaban hukumar kare bayanai ta Kungiyar tarayyar Turai don ta mutunta dokokin EU.

WhatsApp ya gabatar da wasu sabbin ka'idoji kan bayanan sirri, wadanda masu suka suka zarge ta da fadada komar tattara bayanai na miliyoyin masu amfani da kafar.