Jamus ta bullo wasu sabbin dokoki ga masu neman izinin zama kasar | Labarai | DW | 29.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta bullo wasu sabbin dokoki ga masu neman izinin zama kasar

Majalisar ministocin tarayyar Jamus ta mika wasu kudurorin dokoki ga majalisar dokokin kasar domin kara hanzarta batun 'yan gudun hijira masu neman mafaka.

Dokokin wadanda za a fara tafka muhawara akan su a zauran majalisar Bundestag a dai-dai lokacin da rahotani ke nuni da cewar kimanin 'yan gudun hijira dubu goma ne a kullu yaumun suke kokarin tsalakawa zuwa Jamus duk kuwa da matakan kan iyakokin da kasar ta tanada.

Dokokin za kuma su samar da wata horaswa ta musamman kan dunkulewar kabilu ga wadanda ke muradin ganin an karbi takardun iznin zaman su a kasar ta Jamus.

Tuni dai kungiyoyin kare hakkokin dan Adam da ke a Jamus suka soki lamirin dokokin da cewar za su take dokokin 'yancin dan adam a kasar.