Jamus ta bukaci Rasha da Turkiya da su kai zuciya nesa | Labarai | DW | 24.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta bukaci Rasha da Turkiya da su kai zuciya nesa

Jamus ta bukaci mahukuntan biranen Moscow da Ankara da su kai zuciya nesa bayan da Turkiya ta harbo jirgin saman yakin Rasha da ke kusa da kan iyakar Syriya.

Minisatan harkokin kasashen wajen tarayyar Jamus Frank-Walter Steinmeier shi ne ya yi nuni da hakan a inda ya kara da cewar:

Muna fata a mataki na farko su tattauna a tsakanin su. Muna fata kasashen za su nuna dattaku.

Kasashen Rasha da Turkiya tana ci gaba da mayar da martani ne a tsakanin su biyo bayan harbo wani jirgin Rasha da Turkiya tayi da tace ya keta ta sararin samaniyar abin da Rashan ta ce samsam ba haka abin yake ba.