1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Scholz na ziyarar aiki a Faransa

December 10, 2021

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya fara ziyarar aiki ta farko a Faransa bayan shan rantsuwar kama aiki a ranar Larabar data gabata.

https://p.dw.com/p/444iB
BM Scholz trifft Emmanuel Macron in Paris
Hoto: Hans Lucas/picture alliance

Shugaba Emmanuel Macron na Faransar ya yi maraba da zuwan sabon shugaban gwamnatin birnin Paris gabanin shugabanin manyan kasashen su fara tattaunawa kan hanyoyin magance matsalolin kasashen turan.Daga cikin batutuwan da shugabannin za su tattauna, har da batun fargabar mamaye Ukraine da karfin soji da Rasha ke barazanar yi da kuma batun sauyin yanayi.