1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na son Chaina ta sa baki ga yakin Ukraine

Abdoulaye Mamane Amadou
May 26, 2023

Kasar Jamus ta yi kira ga Chaina ta kara wa kawarta Rasha matsin lamba, domin ta gaggauta dakatar da yakin da take gwabzawa a makwabciyarta Ukraine tare da janye dakarunta.

https://p.dw.com/p/4RrZY
Deutschland | Bundeskanzler Olaf Scholz
Hoto: Matthias Schrader/AP Photo/picture alliance

Babban jami'i a ma'aikatar harkokin wajen Jamus Andreas Michaelis ne ya bayyana a yayin wata ganawarsa da manzo na musamman na kasar Chaina a lokacin da ya yada zango Berlin, a ci gaba da zagayen wasu kasashen Turai, kafin ya isa a birnin Moscow.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamus Christian Wagner, ya ce a tsawon tattaunawarsu da Li Hui, takwaransa na Jamus ya nanata batun dakatar da yakin a Ukraine, inda Jamus na son ganin Chaina ta yi amfani karfin fada ajin da ta ke da shi ga gwamnatin Moscow da ta jingine makamai.