1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus na son daidaito a rabon 'yan gudun hijira

Binta Aliyu Zurmi
July 7, 2020

Ministan harkokin cikin gidan Jamus Horst Seehofer na mai kira ga takwarorinsa na kungiyar tarayyar Turai da cewa lokaci ya yi da za a tsaida matsaya dangane da batun raba 'yan gudun hijira.

https://p.dw.com/p/3evZt
Berlin | Pressekonferenz: Horst Seehofer
Hoto: Getty Images/J. Hayoung

Da yake jawabi a wani taron da ya gudana tsakaninsu ta kafar bidiyo a wannan Talata, ministan ya ce dukka kasashen da ke cikin wannan kungiya ya kamata kowace kasa ta dauki nata kason. Ministan ya kara da cewa Jamus ta dade tana neman daidaito a kan batun 'yan gudun hijirar da ke jibge a kasashen Malta da Italiya da Girka amma har yanzu sauran kasashe sun ki amincewa.

A wata tattaunawar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na AFP, Mista Seehofer ya ce da an ceto wani jirgi daga teku a kan kira kasashe a sanar da su ko za a sami masu son daukar su. A baya dai kasar ta Jamus ta dauki dimbin 'yan gudun hijira da yawancinsu suka fito daga kasar Siriya.