Jamus: Muhimmancin tallafa wa kasar Mali
April 7, 2017Ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel da takwaransa na Faransa Jean-Marc Ayrault sun kai ziyara a garin Gao da ke arewacin kasar Mali don duba irin gudummawar da kasashensu ke bayarwa wajen tabbatar da tsaro da kyautata zaman al'uma a yankin mai fama da rikice-rikice 'yan tarzoma.
A lokacin da yake magana da manema labari a wannan Juma'ar, ministan harkokin wajen Jamus Sigma Gabriel ya ce aikin tawagar kasa da kasa a Mali yana da muhammanci ga yankin da ma nahiyar Turai baki daya.
Ya ce:
"Wannan yanki babbar tunga ce ta rikice-rikice, musamman ta'addancin da ke haddasa zaman hijira da kaurar jama'a. Mali kasa ce kuma mai fama da matsanancin talauci, inda matasa ke rasa makoma ta rayuwa, saboda haka ya zama wajibi mu taimaka. Kyakkyawar alama ce yanzu yadda aka samu hadin kai a Turai musamman tsakanin Jamus da Faransa bisa manufar kawo dauki."