1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Jamus ta yi tir da kyamar Yahudawa

Abdullahi Tanko Bala
May 19, 2021

'Yan majalisar dokokin Jamus sun yi kakkausar suka ga lamuran nuna kyamar Yahudawa a lokacin wata muhawara a majalisar dokoki ta Bundestag kan tashin hankalimn da ke faruwa tsakanin Israila da Falasdinawa.

https://p.dw.com/p/3tdfB
Bundeskanzleramt in Berlin
Hoto: Christoph Hardt/Geisler-Fotopres/picture alliance

A yayin zanga zangar adawa a fadin kasar a game da abin da ke faruwa tsakanin Israila da Falasdinawa 'yan sanda sun tarwatsa gangamin nuna kyama ga Yahudawa da kuma tsaurara mnatakan tsaro a wuraren ibadar Yahudawa.

Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya bukaci daukar tsauraran matakai akan masu akidar nuna kyamar Yahudawa da kalaman kiyayya da kuma masu haddasa tarzoma.

Ya kuma yi kiran kawo karshen hare hare akan Israila tare da bukatar tsagaita wuta da kuma yin tattauna kai tsaye tsakanin Israila da Falasdinawa don samun masalaha