1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus da Turkiyya sun karfafa huldar dangantaka.

Abdullahi Tanko Bala
September 29, 2018

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kammala ziyarar da ya kawo Jamus tare da bude wani katafaren masallaci mafi girma a birnin Kolon.

https://p.dw.com/p/35iXv
Angela Merkel Recep Tayip Erdogan G20 Hamburg
Hoto: Getty Images/M.Kappeler

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kammala ziyarar kwanaki uku da ya kawo nan Jamus inda ya gana da shugabar gwamnati Angela Merkel. Shugabannin biyu sun tattauna yadda za su bunkasa dangantakar tattalin arziki a tsakanin kasashensu. 
Ziyarar ta shugaban na Turkiya Recep Tayyip Erdogan zuwa Jamus ta kasance cike da cece-kuce da kuma dambarwa ta diflomasiyya. Kasashen biyu dai sun dade suna zaman tankiya kan batutuwa da dama a 'yan shekarun baya bayan nan musamman kan batun daure wani dan jarida dan kasar Jamus.

Berlin Demonstration bei Staatsbesuch Erdogan
Zanga zangar adawa da Erdogan a BerlinHoto: Getty Images/S. Gallup
Deutschland Recep Tayyip Erdogan, Präsident Türkei & Angela Merkel, Bundeskanzlerin
Angela Merkel da shugaba Erdogan Hoto: Reuters/F. Bensch


Sai dai a wannan ziyara kasashen biyu sun nemi karfafa dangantaka da huldar tattalin arziki a tsakaninsu. Kasashen biyu dai sun fahimci muhimmancin da kowanensu yake da shi. Yayinda ga kasar Jamus Turkiyya ke zama jigo wajen cimma manufar kungiyar tarayyar Turai na takaita kwararar 'yan gudun hijira zuwa cikin Turai, a nata bangaren Turkiyya na fatan samun hadin kan Jamus da sauran kasashen Turai domin bunkasa tattalin arzikinta. Dangantakar da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kara tabbatarwa.
"Ta ce jamus na da sha'awar ganin tattalin arzikin Turkiyya ya samun ci gaba, babu shakka mun tattauna kawancen tattalin arziki wanda ya hada da ziyarar ministocin Turkiyya gabanin ziyarar shugaban kasar. Wannan ne ma ya sa muka dora da nasarrorin da muka samu a yau, kuma ministan tattalin arziki Peter Altemeier zai kai ziyara Turkiyya inda a karon farko za a shirya taron tattalin arziki na hadin gwiwa a tsakanin kasashenmu biyu da kuma bunkasar makamashi."


Da yake nasa tsokaci shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan yace sun yi tattaunawa mai armashi da shugabar gwamnati Angela Merkel.

"Yace a tattaunawar mu da shugabar gwamnati mun duba bukatar samar da ginshikin tattalin arziki mai karfi. A shirye muke mu tunkari kalubalen da muke fuskanta na tattalin arziki a saboda haka yake da muhimmanci mu sami hadin kan Jamus  domin samar da cigaba."
Ziyarar da shugaban Turkiyan ya sami karramawa da kyakkyawar tarba daga shugaban kasar Jamus Frank Walter-Steinmeier wanda ya shirya masa faretin ban girma. A jawabinsa shugaban kasa Steinmeier ya yi amfani da wannan dama wajen baiyana damuwa game da Jamusawa da ake tsare da su a Turkiyya.

Deutschland Recep Tayyip Erdogan, Präsident Türkei | mit Bundespräsident Steinmeier
Erdogan da shugaban kasar Jamus SteinmeierHoto: Reuters/R. Krause


A hannu daya dai shugaba Erdogan yace ziyarar tasa ta yi nasara. Haka kuma shugaban ya kuma bude wani kasaitaccen masallaci a birnin Kolon irinsa mafi girma a Turai. Sai dai kuma a waje guda dubban jama'a masu sukar lamirinsa sun gudanar zanga zangar adawa da ziyararsa. 'Yan sanda sun tsaurara matakan tsaro domin tabbatar da nasarar ziyarar cikin kwanciyar hankali da lumana.