1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Jam'iyyar CDU ta sami karin tagomashi

June 7, 2021

Bisa dukkan alamu jami'iyar CDU ta Shugaba Merkel ta sami nutsuwa da kwanciyar hankali bayan samun nasara a kuri'un da aka kada a zaben yakuna gabanin babban zabe na kasa.

https://p.dw.com/p/3uVwK
Landtagswahl Sachsen-Anhalt - CDU
Hoto: Bernd Von Jutrczenka/dpa/picture alliance

Jam'iyar ta CDU karkashin sabon shugabanta Armin Laschet ta sami nasara da kashi 37 cikin 100 na kuru'un da aka kada a Saxony-Anhalt a ranar lahadi, yayinda jam'iyar AFD ke da kashi 21 cikin 100. Ita kuwa jami'iyar The Greens da ke kokarin shan gaban CDU ta sami kaso mai sanyaya gwiwa wato kashi 6 kacal cikin 100 na kuri'un.  

Sakamakon zaben da aka samu a tsohuwar jihar ta gabashin Jamus wani kwarin gwiwa ne ga Laschet da ke son zama shugaban gwamnatin Jamus a zabe mai zuwa na ranar 26 ga watan Satumbar wannan shekarar.