Jamus: Ba sabuwar yarjejeniya da Girka | Labarai | DW | 10.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Ba sabuwar yarjejeniya da Girka

Wolfgang Schaeuble ministan kudin Jamus ya ce babu gaskiya a rahotannin da ke fita cewa kasar Girka ta shiga sabuwar tattaunawa da kasashen da ke binta bashi.

Berlin Steuerkonferenz 2014

Wolfgang Schaeuble: Ministan harkokin kudin Jamus

Ministan harkokin kudin Jamus Wolfgang Schaeuble a yau Talata ya bayyana cewa babu wani sabon shiri kan tallafa wa tattalin arzikin Girka inda ya ce ya zama wajibi a fara daddalewa akan shirin da aka fara karon farko.

Da yake jawabi a wajen taron ministocin harkokin kudade daga kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 da ke wakana a birnin Istanbul na kasar Turkiya ya bayyana cewa babu kanshin gaskiya a rahotannin da ke fita cewa kasar Girka ta shiga sabuwar tattaunawa da kasashen da ke binta bashi.

Ya ce babu wata sabuwar yarjejeniya da suka shiga, tuni suna da shirin da suke kansa a yanzu za kuma a sake tattaunawa a kansa a taron ministoci na kungiyar ta EU da za a yi anan gaba cikin wannan mako.