1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 698 sun mutu a yini guda da corona a Jamus

Abdourahamane Hassane
December 17, 2020

A karo na biyu an samu addadi mafi yawa na wadanda suka mutu tun lokacin da aka soma yin annobar coronavirus a Jamus.

https://p.dw.com/p/3mrpq
BdT Deutschland Kaserne in Norddeutschland soll zentrales Impfstofflager werden
Hoto: Hauke-Christian Dittrich/dpa/picture alliance

Cibiyar bincike ta Robert Koch ta ce a cikin yini daya an samu mutane 698 wadanda suka mutu a sanadin cutar yayin da aka samu sama da mutane dubu 26 sabbin kamuwa. A yau aka shirya shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta tattauna ta hanyar bidiyo da jami'an kamfanin BionNTech na Jamus wanda bisa hadin gwiwa da Pfizer na Amirka suka fito da rigakfin coronar. Ana sa ran a  cikin sabuwar shekara mai kamawa za a fara yin rigakfin na corona a Jamus.