Jamus: An samu dan Siriya da laifin garkuwa | Labarai | DW | 16.10.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: An samu dan Siriya da laifin garkuwa

Jami'an 'yan sanda a birnin Kolon na kasar Jamus sun bayyana mutumin da yayi garkuwa da wata mata a ranar Litinin din data gabata da cewar dan asalin kasar Siriya ne wanda ke zaman gudun hijira a Jamus.

Babban Jami'in 'yan sandan birnin Kolon Klaus-Stephen Becker ya shaidawa manema labarai yadda mutumin yayi yunkurun kunna wuta a gidan abinci na McDonald dake babbar tashar jirgin kasan birnin na Kolon kafin yayi garkiwa da wata mace dake tsaka da aiki a wani kantin sayar da magunguna. Binciken da jami'an tsaro suka gudanar ya tabbatar da cewar mutumin wanda ya shigo Jamus a shekara ta 2015 kuma a halin yanzu yake da shaidar ci gaba da zama a kasar har zuwa shekara ta 2021 na da alaka da kungiyar ta'adda ta IS.

A wani sabon labarin kuma mataimakiyar shugaban hukumar 'yan sanda a Kolon Miriam Brauns ta bayyana cewar duk da jami'an tsaro sun yi nasarar harbinsa a lokacin da suke yunkurin cafke shi, a halin da ake ciki yana taimakawa jami'an tsaro da bayanai.