Ana sa ran duban jama'a za su fito yin zanga-zanga a wasu jihohi dabam-dabam na tarayyar Jamus don nuna rashin jin dadinsu kan matakan takaita zirga-zirga da hukumomi ke dauka don dakile Covid-19.
Rahotanni daga sassan kasar Jamus sun ce masu akidar tsananin kyamar baki da dama ne ake hasashen za su fito don yin zanga-zangar a karshen wannan mako ciki har da jihohin Munich da Dortmund da ma babban birnin kasar wato Berlin.
Akalla mutun dubu biyar ne suka fito yin boren a baya a birnin Stuttgart, duk da matakin hana yin duk wani taron da ke tara jama'a da hukumomin kasar suka yi a baya.
Masu boren dai na ci gaba ne da nuna kyama kan matakan gwamnatin kaar da suka kira na hana walwala da 'yan cin jama'a.