Jam'iyyar AfD ta zabi jagororin zabe | Labarai | DW | 23.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam'iyyar AfD ta zabi jagororin zabe

Zaben 'yan takara dai na zuwa ne bayan zama na kwanaki biyu da wakilan jam'iyyar 600 suka yi a birnin Cologne na Tarayyar Jamus.

Jam'iyyar masu kin baki ta AfD a Jamus ta zabi Alexander Gauland da Alice Weidel a matsayin wadanda za su ja ragamar jam'iyyar a kokari na danganawa da zauren majalisar dokikin Jamus a zabe gamagari da za a yi a kasar nan gaba a wannan shekara, wadannan 'yan takara dai na zuwa ne bayan zama na kwanaki biyu da wakilan jam'iyyar 600 suka yi a birnin Cologne na Tarayyar Jamus.

Gauland dai ana masa kallo a matsayin dan kishin kasa yayin da Weidel ke zama masaniya a fannin tatalin arziki mai sassauncin ra'ayi. An dai kada kuri'ar ne don zabin 'yan takarar cikin sirri.