Jami’an diplomasiyya daga ƙasashen Turai na ci gaba da shawarwari a Isra’ila. | Labarai | DW | 23.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jami’an diplomasiyya daga ƙasashen Turai na ci gaba da shawarwari a Isra’ila.

Manyan jami’an diplomasiyya daga ƙasashe 3 na Ƙungiyar Haɗin Kan Turai na ci gaba da yunƙurin da ake yi a huskar diplomasiyyan, don kawo ƙarshen yaƙin da ake ta gwabzawa tsakanin dakarun Isra’ila da mayaƙan Ƙungiyar Hizbullahi.

Ministoci daga Faransa, da Jamus da Birtaniya sun yi shawarwari daban-daban da jami’an Isra’ila yau a birnin ƙudus, gabannin isowar sakatariyar harkokin wajen Amirka, Condoleeza Rice a yankin.

Ƙasashen Turai dai, sun fi sukar Isra’ila game da wannan yaƙin, a daura da Amirka, wadda take daddage wa duk wani kira na tsagaita buɗe wuta. Ita dai Amirkan tana zargin Hizbullahi ne da janyo wannan rikicin.

A halin da ake ciki yanzu, wata jaridar Isra’ilan ta ce jami’an gwamnatin ƙasar sun yi imanin cewa, suna da cikakken goyon bayan Amirka wajen ci gaba da farmakinsu a Lebanon har tsawon mako ɗaya nan gaba.

A ran laraba mai zuwa ne dai ministocin harkokin waje daga ƙasashen yamma, da na kasashen Larabawa za su yi wani taron gaggawa a birnin Rom don tattauna rikicin na Gabas Tsakiya. Kafin ƙarshen wannan taron dai masharhanta na ganin cewa, babu wani matakin da za a ɗauka a fagen siyasar ƙasa da ƙasa, a kan wannan rikicin.