IS: Rasha ta bawa Iraki da Siriya makamai | Labarai | DW | 22.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

IS: Rasha ta bawa Iraki da Siriya makamai

Mahukuntan Rasha sun ce sun baiwa Iraki da Siriya makamai don taimaka musu a yakin da suke yi 'yan kungiyar nan ta IS da ke son kafa daular Islama a kasashen biyu.

Ministan harkokin wajen Rasha din Sergei Lavrov ne ya ambata hakan, sai dai bai yi karin haske ba kan irin makaman da Rasha din ta baiwa kasashen biyu amma dai ya ce sun yi hakan ne don magance irin aiyyukan da suke yi a kasashen da ma wanda ake fargabar za su iya yi a Turai.

Rasha da ke cikin jerin kasashen da ke fuskantar barazana ta masu kaifin kishin addini na daga cikin kasashen da ke bada gagaruma wajen kawo karshen kungyiar ta IS.