IS na kara samun galaba | Labarai | DW | 06.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

IS na kara samun galaba

Kungiyar IS ta kafa tutarta a kan wani dogon gini da ke gabashin garin Kobani, garin da 'yan kungiyar ke ta gwabza fada tsakaninsu da dakarun Kurdawa.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters da kuma ofishin rundunar sojojin Turkiya sun ruwaito cewa kungiyar ta IS ta kafa tutarta a gabashin garin na Kobani da ke kan iyakar Siriya. Wani jami'in soja na kasar Turkiya da ya nemi a sakaya sunansa ya sanar da cewa ana iya ganin bakar tutar 'yan IS a daf da inda suka gwabza kazamin fada tsakaninsu da dakarun Kurdawa a garin na Kobani. Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Amirka ke ci gaba da jagorantar kasashe masu yawa wajen yin barin wuta a yankunan da 'yan IS din suka mamaye a kasashen Siriya da Iraki, a kokarin da suke na dakile ayyukansu.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Pinado Abdu Waba