1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta sake kwace jirgin dakon mai

Abdul-raheem Hassan
August 4, 2019

Kwamandan sojojin kundumbala na juyin juya halin Kasar Iran na zargin jirgin da fasakobri kusan lita dubu 700 na man fetir zuwa wasu kasashen Larabawa.

https://p.dw.com/p/3NJuQ
Iran setzt britischen Tanker in der Straße von Hormus  fest
Hoto: picture-alliance/dpa/AP Photo

Sojojin ruwa na Iran sun tabbatar da tsare wani wani jirgi ruwa mai dakon man fetur na kasar waje a yankin Gulf, wannan shi ne jirgin dakon mai na uku da jami'an tsaron gabar ruwan Iran suka tsare a baya-bayan nan ciki har da tankar dakon man Kasar Birtaniya.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Amirka ta gaza hada kawancen kasa da kasa a yankin Gulf, domin kare jiragen ruwan da ke dakon man fetIr masu ratsawa ta mashigin ruwan Hormuz a tekun fasha, Jamus na cikin kasashen da suka yi hannun riga  da tayin shiga kawance.