Iraki tana kara samun taimako | Labarai | DW | 12.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iraki tana kara samun taimako

Faransa za ta taimaka wa Iraki wajen yakan masu tada zaune tsaye

Shugaban Faransa Francois Hollande ya tabbatar da shirin kasar na ba da gudumawa ga kasar Iraki, domin dakile kungiyar da ta kafa daulan Islama, wadda ake zargi da aikata miyagun laifuka.

Hollande ya shaida wa sabon Firaministan kasar Iraki Haidar al-Abadi haka, lokacin da ya kai ziyara Bagadaza babban birnin lasar ta Iraki a wannan Jumma'a, inda shugabannin suka gudanar da taron manema labarai. Shugaba Hollande ya ce nan gaba kadan Faransa za ta yanke hukunci kan hanyoyin da za ta taimaka wajen katse hanzalin masu kaifin kishin Islama.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba