Inganta rayuwa don yakar ta′adanci a Sahel | Siyasa | DW | 17.10.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Inganta rayuwa don yakar ta'adanci a Sahel

Shugaban Jamhuriyar Nijar da ke jagorancin kungiyar G5 sahel ya bai wa kwamitin zartarwar kungiyar umarnin samar da tsarin kyautata rayuwar jama'a a yankin Sahel da ke fama da ta’addanci maimakon amfaani da karfin soja.

Hukumomi sun ce za a ci gaba da mayar da hankali ga samar da hanyoyin ruwan sha da kayayyakin more rayuwa ga matasa domin magance ta'addancin a yankin na Sahel baya ga tashoshin rediyo da ke shirin wayar da kai game da matsalolin ayyukan ta'addancin, lamarin da masu sharhi ke ganin na iya kawo sauyi ga halin da yankin na sahel yake ciki. Tun a cikin watan Fabarairun shekarar 2014 ne dai shugabannin kasashen Burkina Faso da Murtaniya da Mali da Nijar da kuma Chadi suka kafa kungiyar farfadowa da raya tattalin arziki da bunkasar kasashen biyar na yankin sahel mai suna G5 Sahel Sai dai kungiyar na fuskantar matsaloli na kyautata rayuwar al'ummar kasashen da ke cikinta da matsalolin tsaro musamman ma ayyukan ta'addanci da ke barazana ga batun daidaita al'amura a yankin, baya ga fatara da talauci da rashin aikin yi ga matasa da ya yi wa yankin na sahel katutu.

Shekaru hudu na kalubale

Sai dai shekaru hudu bayan kafa kungiyar batun yaki da ta'addancin ne kadai shugabannin kasashen suka fi mayar da hankali akai tare da kai su ga kafa wata runduna ta musaman domin yakar 'yan ta'addan da suka yi tunga a yankin, ta hanyar yaki da karfin askarawan soja akalla 5,000, batun kuma da ga alama a yanzu ya fara sauyawa, inda hukumomin koli na kasashen kungiyar musamman ma shugabanta na zartarwa a yanzu Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar suka bai wa hukumar zartarwa ta kungiyar umarnin sake duba wasu mahimman hanyoyin yaki da ayyukan ta'addancin maimakon rungumar karfin soja kawai.

Mali - Französische und malische Truppen töten in Mali 30 Dschihadisten (Getty Images/AFP/D. Benoit)

Sojoji na yakar ta'addanci a yankin Sahel

Bukatar daukar sabon mataki

Malam Mamane Sambo Sidikou Babban jami'in zartarwa ne na hukumar ta G5 sahel, ya ce domin tabbatar da tsaron yankin mai dorewa dole ne sai an shimfida yarda tsakanin soja da al'umma kana dole ne sai al'ummomin da ke yankunan sun hakikance kasancewar gwamnati a wuraren da suke, domin kuwa a duk lokacin da babu kulawa ta fannin lafiya ilimi ko kananan ofisoshin 'yan sanda, to hakaika ana iya cewar babu gwamnati a wajen. Yanzu hakan dai kungiyar ta ce ta tashi haikan domin kakkafa hanyoyin kara kyautata rayuwar jama'a da zai kai ga kawo karshen radadin matsalolin na tsaro, maimakon aiki da karfin soja kawai. A farkon watan Disambar wannan shekarar ne dai kungiyar ta G5 za ta gabatar da taron neman tallafi daga masu hannu da shuni don tabbatar da wadannan tsare-tsaren da take son runguma domin kawo ci-gaba. Sai dai a cewar wasu masu sharhi game da batutuwan tsaro kamar Alkassoum Abdourahman tun da jimawa ya kamata a ce kungiyar ta G5 ta yi irin wannan tunani.

Sauti da bidiyo akan labarin