1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Indiya ta kulla cinikayyar jiragen sama na yaki da Rasha

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
October 28, 2025

Amurka da aminanta na yamma sun soki lamirin manufofin Indiya ta fannin alakarta da Rasha, tun bayan da ta fara mamayar Ukraine a 2022

https://p.dw.com/p/52hsl
Firaministan Indiya Narendra Modi tare da shugaba Vladimir Putin na Rasha
Hoto: Alexander Kazakov/Sputnik/REUTERS

Kasar Indiya ta sanya hannu kan yarjejeniyar cinikayyar jiragen sama na yaki da kamfanin kera makamai na Rasha da ke fama da takunkumi daga Amurka da kuma Turai, lamarin da ka iya fusata manyan kasashen yamma.

Ministan harkokin tsaron Indiya Rajnath Singh, ya wallafa wani sako a shafinsa na X cewa kasarsa ta cimma wannan gagarumar nasara ta sayayyar makaman yaki wadda za ta bunkasa fannin samar da aikin yi da kuma dogaro da kai a kasar.

Karin bayani:Shugaba Zelenky ya gana da shugabannin Indiya da Saudiyya

A baya dai Amurka da aminanta na yamma sun soki lamirin manufofin Indiya ta fannin alakarta da Rasha, tun bayan da ta fara mamayar Ukraine a cikin shekarar 2022, inda suka yi kira gare ta da ta yi biyayya ga muradinsu na kakabawa Rasha takunkumai.