1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutum kusan dubu 80 sun kamu da COVID

Zainab Mohammed Abubakar
August 30, 2020

A wannan Lahadin ce Indiya ta kafa tarihi na samun mafi yawan sabbin mutane kusan dubu 80 ne suka kamu da coronavirus a rana guda.

https://p.dw.com/p/3hl9P
Indien Mumbai | Coronakrise
Hoto: Imago Images/Hindustan Times

Rahotanni na nuni da cewar cikin tsukin sao'i 24 kacal, mutane dubu 78, 761 sun kamu da wannan cuta.

Indiya da ke da yawan al'umma biliyan1.3 dai, na zama kasa ta uku a jerin wadanda suka fi yawan masu COVID 19 bayan Amurka da Brazil, inda kawo yanzu mutane miliyan 3 da dubu 500 suka kamua kasar.

A ranar 17 ga watan Yuli ne dai, Amurka ta sanar da mafi yawan sabbin kamuwa da cutar na mutane dubu 77,638 cikin tsukin sao'i 24, a cewar alkaluman kamfanin dillancin labarun Faransa na AFP.

Jamus a daya hannun Jamus  nada yawan masu corona 241,771, daga cikinsu 9,295 sun rasa rayukansu.

A yanzu haka dai sama da mutane miliyan 25 ne suka kamu da cutar ta COVID 19 a fadin duniya. Tun bayan barkewar wannan annoba dai, wannan shi ne karon farko da  mutane kusan dubu 80 suka harbu da cutar a rana guda.