Ibrahim Gambari ya koma Rangoon wata guda bayan murƙushe zanga-zangar ƙyamar gwamnati | Labarai | DW | 03.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ibrahim Gambari ya koma Rangoon wata guda bayan murƙushe zanga-zangar ƙyamar gwamnati

Wata guda bayan murkushe zanga-zangar lumana ta kyamar gwamnatin mulkin sojin kasar Burma ko Myanmar, a yau wakilin MDD na musamman Ibrahim Gambari ya isa kasar. A wannan ziyarar wadda ita ce ta biyu da ya kaiwa kasar cikin wata guda, wakilin na MDD zai gana da shugabannin gwamnatin soji a fadar gwamnati dake yankin Naypyidaw. Ziyarar ta Alhaji Gambari zuwa kasar ta zo ne a daidai, lokacin da ake takaddamar MDD da kuma gwamnatin sojin Burma wadda a jiya juma´a ta bayyana babban jami´in MDD a kasar Charles Petrie da cewa wani mutum ne da ba´a bukatar sa a cikin kasar. Shi dai Petrie ya fito karara ya soki lamirin gwamnati da kuma matsalolin talaucin da suka yiwa jama´a katutu.