An kashe yara guda bakwai kana wasu biyar suka jikkata a wani harin kuskure ta jiragen sama na yaki da rundunar sojojin Najeriya ta kai a kan iyaka da Nijar a Jihar Maradi.
Gwamna Jihar Maradi Chaibu Abubakar ya ce harin wanda dakarun Najeriya suka kai bisa kuskure kan zaton cewar 'yan fashin daji ne, ya faru a garin Nachade da ke a yankin Madarounfa da ke kan iyaka da Najeriya. Yankunan da dama da ke cikin Jihar Maradi wadanda ke kan iyaka da Najeriya na fuskantar hare-hare na 'yan fashin dajin.