Harin kunar bakin wake a Kamaru | Labarai | DW | 11.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake a Kamaru

A kalla fararen hula bakwai ne suka rasa rayukansu sakamakon wani harin kunar bakin wake a garin Kolofata da ke yankin Arewacin kasar Kamaru.

Harin kunar bakin wake a Kolofata na Kamaru

Harin kunar bakin wake a Kolofata na Kamaru

Yankin Arewacin Kamaru dai ya yi kaurin suna da hare-haren ta'addanci daga kungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a makwabciyarta Tarayyar Najeriya. Wata majiyar tsaro daga yankin ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane takwas ciki kuwa har da wanda ya kai harin, ko da yake majiyar ba ta bayyana jinsin wanda ya kai harin ba. Wannan ne dai karo na biyu da garin na Kolofata ke fuskantar hare-haren ta'addanci wanda ake dora alhakinsa a kan kungiyar Boko Haram da ta addabi Tarayyar Najeriya da makwabtanta.