Kolofata wata karamar hukuma ce da ke cikin yankin Arewa mai nisa na Kamaru.
Daya ne daga cikin garuruwa da suka fi fuskantar hare-haren daga 'yan Boko Haram a Kamaru. A ranar 12 ga watan Janairun 2015, sai da 'yan bindiga suka kai hari a kan barikin sojoji da ke Kolofata.